Kwana Darin Gwamna A.A Sule LINK
Ta ce tunda ba bani zai yi ba ai batun hanawa ma bata taso ba, shi fa yanda na kula koma menene kije kiyi amma kada ki tambaye shi, sukansu kishiyoyin nawa da yake sonsu baya musu komai, amma don rashin tunani suna nan suna ta zabga gasar haihuwa,yaran bacin kirki bare sutura, karatu kuwa sai dai na zagi ashar kam, kwando-kwando za ki ga dan karamin yaro yana saukewa, gaskiya 'yan gidanmu su ne suke bata ma zage zagi suna, shin haka kowane gida suke yi? Hajara tace a'a akwai dai masu yin amma ba duka ba.. Cike da farin ciki tabar gidan hajara, ta samu Bilkisu da yan kannanta a cikin daki, tana koya musu darasin lissafi, nan ta zayyane ma Bilkisu komai, Bilki ta ce mamanmu ki bari ni nayi aikin in an samu, ta ce a'a nafi soe ni in yi bana son kije ki bata ma masu gidan har su sallame ki, bukatarmu ya zama bata biya ba. tace mamanmu amma kinsan bana fada ko? tace na sani maigado, amma ki bari sai dai an samu din kisan ke yarinya ce ba kowane abu ne zaki iya yin shi ba. Sallamar Mansura ta katse su, suka amsa ta shigo kusa da mamanmu ta zauna sannan tce mamanmu ina kwana? Suja gaisa ta dubi Bilkisu tace "Bily ya dai, yaushe zaki fara shiga school ni dai on monday zan fara zuwa. Bilki tace ni kam ba rana Mansu, kila ma sai second term. Mansura tace akan me? Tace kudi, mamanmu tace kin san ko mai yanzu sai da kudi ana cewa ne dai makarantar gwamnati amma suma duk shegiyar darin ce ga kudin motan zuwa makaranta kullum mansura tace bari Abbanmu yazo week end zan gaya masa. Bilki har suna hada baki da mamanmu, a'a kar ki yi masa magana shima yana ji da nasa iyalin. Mansura tayi shiru, amma a ranta ta raya sai ta fada mashi... Haka kuwa yana dawowa ta gaya mishi, ya tambaye ta ko njawa suke nema? Ta ce ya basu kowanne ita dai bata sani ba, kuma ta san ko ta tambaye su ba zasu fada ba. Dubu goma ya bata yace, gashi ki basu." sai da ta kai kudin mamanmu da yaranta suka je suyi godiya,Bilki kuwa sai da tayi kukan murna, sannan tana ta mamakin dama da gaske ne akwai iyaye masu yiwa 'ya'yansu hidima? Ba sabanin iyayansu mata da wahala? Cikin nasara ta shiga j.s.1 mansura kullum in za su je makaranta sai ta saka direbansu ya biyo sun dauki Bily, sunan da ta ke kiran bilkisu kenan, ita kuma Bilki tace Mansu, wani abin da yake kara ba Bilkisu mamaki shi ne, yanda mafarkin Yarima ke kara yawaita a gare ta, ko gyangyadi take sai ta yi bare barcin dare. saboda sabon da suka yi har ta saka mishi Yarima aboki, shi ko yana kiranta Beauty, tana son sanar da mamanmu amma tasan mamanmu zata ce shirme ne, shi yasa take bar ma cikinta don ko mansu bata taba ba wa lbri ba. cikin haka hajara tazo ta ce, an samu aiki. Mamanmu tace ai ko zan yi,
Kwana darin Gwamna A.A Sule
Nan Yarima ya yiwa mahaifin bayanin cewa matsalar ta kayan aiki ne,cewa yayi shi zai bada kudin kayan aikin ko nawa ne. Yarima cikin satin yayi aike kayan suka iso, ya bukaci hoton yarinyar lokacin da take lafia,Allah cikin ikonsa sai gashi aiki ya kammalu zuwa wasu kwanaki ya bude aikin,an sha mamaki ganin fuskar yarinyar ta samu,shi kansa sam bai zaci aikin zaiyi kyau haka ba,sai dai kamanninta sun dan canza kadan,sai tafi da kyau ma,wannan aikin ya jawo daukakar sunan Yarima a fadin kasar nan inda asibitoci masu zaman kansu dana gwamnati suka yi ta gayyatar Yarima ire-iren wadannan aikin har ya kasance baya samun isasshen lokacin zama a gida,wani lokacin kuma cikin dare ne zaki ga anyo masa waya ana nemansa Emergency. Tiyata da makamantansu,abin yana cin ran Bily,domin aikinsa yanzu yasa bata samun kulawa sosai zata tsaya tayi gayun da kananan kaya ne da shaddodin ne zuwa lesuka,atamfofi amma wani lokacin ma har ta cire tasa kayan bacci bai dawo ba,yana dawowa kuma duk a gajiye da yayi wanka shikenan zai kwanta sai bacci.yau ma kusan kwana tara kenan haka na faruwa,domin wannan karon har asibitin Ibadan yaje yayi kwana biyu.yau tana sa ran sati ne da Lahadi dole yana gida,tunda yayi sallar asubahi ya koma ya kwanta,tara daidai ta tashi ta shi ta koma dakinsa ta zauna kusa da fuskarsa tace,abban son bazakayi wanka ba?Yayi mika barni inyi bacci beauty jiya nayi aiki sosai,mutum shidda na fede,tace shikenan mu kuma yanzu aiki yafi mu, ya tashi zaune yana kallonta,kamar yaya?Ta dubesa to yanzun fa bakada lokacinmu,yau kana aiki nan gobe kana aiki can.ya matso kusa da ita ya jawota jikinsa wannan aikin fa in kinyi tunani beauty dalilinsa ne na bata shekaru ina karatu,kuma an samu Allah ya taimakeni inda zaki lura aikin taimako ne,kin sani na fiki son hutu tunda kika ga sai mu kwanta mu tashi ban lalubeki ba kin san wani aikin yasha gaban wani Amma kiyi hakuri ko wane dan adam yanacin zamaninsa ne,yanzun lkcina ne akan aikina wata rana sai kiga an sami wanda ya doke ni,to ba kya ganin gara nayi amfani da damata da lokacina in samu aljannata, nasan dama ke ba makawa in dai miji ke daga kafa a shiga tawa dama a dage take shikenan sai ki jagoranci sauran matana na gidan aljanna,tayi driya to kwanta ka huta,yace a鈥榓 na fasa yanzun 鈥榶ar hira zamuyi irin wadda muka kwana biyu bamuyi ba, tace yau ai kana gida harda irin wadda bamu taba yi ba duk zamuyi. Yanzun dai kwnta kurum kayi baccinka,kuma matseta yayi sai sukaji kiran waya,ya kalleta fuskarta daure ya dauki wayar yana yi mata dariya,bataji kome aka ce masa ba ta daiji yace zanzo to nan da 10.ya fada tare da kallon agogo,ta mike zata fita yace zo nan gimbiya bana fushi bane maigadon zinari,marasa lafia na zan duba ance biyu daga cikin wadanda nayiwa fida basu farfado ba,amma ina ganin ba wata matsala bace,kafin goma zasu farka,tace um ai kai nasan in kaje sai kuma na ganka,yace shirya muje tare ta dubesa da gaske? Yace na taba cewa ki shirya muje?Tace a鈥榓 ta fita ta zuwa dakinta cikin doguwar rigar shadda ta fito aslin soly ja,takalmi da jaka da gyale farare,hatta abin hannunta fari ne, shi ko farin yadi ne mai shara-shara wnda kana gani kaga yadin manya,salon daurin dankwalin Bily ya burgesa yace kai beauty dafa naso inyiwa kaina asara tayi fari tareda cewa ko?Yace ina son? Dashi zamu dakkosa in kina cigaba da min wannan farin tafiyar tamu zata iya fasuwa,tace yana hannun Asabe,yace amsosa mukadai zamu baki so muyi 鈥榶ar hira irinta sirri?Tace to muje in amshesa sai muyi ma Umma sallama.Son yayi kyau cikin wandon jeans,pink da fara kar din shirt, takalminsa pink da 鈥榶ar safa fara,shine ya dauki son din suka yiwa Umma sallama da cewa sunje asibiti,hakan yayi matukar birge Umma,suka nufi katuwar jeep dinsa tace tunda nazo gidannan yau ne rana ta farko da na shiga unguwar nan da rana kamar yanzun,ya dubeta yanzun ma shahada nayi don fa ni bana son ana kallemin ke,tace um wata rana inna kallemu sai inga tamkar masoya? Ya dubeta yaya ake gane mutum ya kamu da so?Tace kaine fa doctor nawa, zaka fini sani yayi murmushi ni ba likitan zuciya bane,kuma ban karanci so ba,kuma bai taba kamani ba,don haka ban san shi ba,tayi shiru yace kin taba so?Ko kuma sanin yanda yake?Tace ban taba so ba,sai dai ina sha鈥榓war aso ni,ina so in sanshi inyishi,da sauri ya dubeta kiyi ma wa? Tace kai mana nawan. Ta cigaba na taba karantawa wani littafi, marubuciyar cewa tayi shi so wani halitta ne wanda da zaran mutum yaga abinda yake so zai shige shi nan take,da zaran ka kamu da son wata baka da sauran nutsuwa,zaka kasance cikin tunanin abin sonka tare da kasancewa da abin son naka duk rintsi duk wuya,Yarima yayi dariya tare da cewa,malamar so kice kinsan so kenan?Tace a鈥榓 naji dai labarinsa amma banyi saba ban kuma sansa ba.suna isowa asibitin shine ya dauki son suka jero duk da cewa Asabar ne asibitin yana cike da mutane,sai kallonsu akeyi ballantana nurse din da suke nan sai kallon Bily sukeyi,a cikin zukatansu suna cewa lallai dole ne Dr. Yrm ya dinga yiwa mata kallon baku yi ba,daf da zasu shiga office dinsa wata Dr. Jamila ta iso tana cewa a鈥榓 Dr. kai da madam ne?Ta amshi son suka shiga office din ta bisu,tamkar ba asibiti ba office din domin ya tsaru(AC)ma kusan guda uku ne tace dama shi dan sanyi ne,gadon dake gefe ne irin wanda marasa lafia kan kwanta kawai zai nuna maka cewa nan office din likita ne.kujerar da aka tanada domin likitan itace ya nuna Bily tare da cewa beauty please sit down,ta zauna tana kallonsa tare da cewa,yau nima nazama doctor. Dr. Jamila ta dubi Bily yaya gajiya madam ya kike? Lafia,inji Bily fuskarta ba walwala tace Dr. Familyn ka masu kyau,yace na gode me kika zoyi asibiti yau Sunday?Tace ina da mara lafia,maman kawata ce ba lafia,yanzun sukayi min waya wai jikinta din ya tashi shine nazo in duba,Allah ya sauwake. 041b061a72